Home Labarai Nasarawa za ta mayar da Almajirai dubu 63 jihohin su

Nasarawa za ta mayar da Almajirai dubu 63 jihohin su

58
0

Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na mayar da Almajiran da ba ƴan asalin jihar ba, ƴan ƙasa da shekara 10 jihohin su.

Kwamishinar harkokin mata ta jihar Halima Labiru ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da ƴan jarida bayan taron majalisar zartarwar jihar a birnin Lafiya.

Jabiru, ta ce kimanin almajirai dubu 63 ne ke gararanba a titunan jihar.

Idan dai za a iya tunawa Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya zartar da wata dokar ɗaurin shekara 10 a gidan ga duk iyayen da suka bar yaran su na bara a kan titunan jihar.

Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta hukunta yaran da ke bara ba, saidai mutanen da ke sanya yaran bara za su ɗanɗana kuɗar su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply