Hukumar da ke kula da kafafen yada labarai ta Nijeriya NBC ta nuna kin amincewarta kan wani sabon shiri na yin garambawul ga dokokin ayyukan yada labaran kasar.
Shugaban hukumar kuma tsohon ministan yada labarai Alhaji Ikra Aliyu Bilbis ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a wajen wani taro da ya yi da manema labarai a Abuja.
Bilbis ya ce kafin kin amincewar hukumar, sai da suka karbi bayanai da ma daukar dogon lokaci wajen tattaro ra’ayoyin masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban na hukumar, inda mafi akasarin su suka nuna rashin goyon bayan su na kin yin garambawul din.
A karshe ya ba da tabbacin cewa hukumar ba ta goyon bayan garambawul din da ministan yada labarai da al’adun kasar nan Alhaji Lai Muhammad ya ce za a yi wa hukumar.
