Hukumar kididdiga ta Nijeriya, NBS, ta kididdige cewa kusan kaso arba’in daga cikin dari (40%) na al’ummar Nijeriya na cikin talauci.
Rahoton yace kusan mutane milyan 82.9 ne ke cikin talauci a kasar da take kusan uwa a Nijeriya Afrika. Rahoton kididdigar na wakiltar binciken da hukumar ta yi a shekarun 2018 da 2019.
An dai alakanta hakan da bunkasar yawan al’umma, ga kuma raunin da tattalin arzikin kasar ke samu.
Majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa idan aka tafi a haka, to kuwa yawan al’ummar Nijeriya na iya kai milyan 400 nan da zuwa shekarar 2050
