Hukumar kula da sadarwa ta Nijeriya NCC ta ce cikin shekaru 5 ta tattara kudin da suka kai darajar Naira bilyan N344.71 kuma ta saka su a lalitar gwamnatin tarayya.
Mataimakon shugaban hukumar Prof Umar Danbatta ya furta haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da sadarwa a Abuja.
A cikin wata takarda daga daraktan watsa labarai na hukumar Dr Ikechukwu Adinde, ta ce Prof Danbatta ya zayyano irin nasarorin da hukumar ta samu a cikin shekaru 5 da suka shude.
Ya ce sashen sadarwa na kasa ya taimaka sosai wajen inganta ma’aunin tattalin arzikin Nijeriya na GDP daga kaso 8.5 zuwa kaso 14.30 daga cikin dari daga 2015 zuwa 2020.
