Abdullahi Garba Jani/dkura
Hukumar shirya jarabawar karshe ta makarantar sakandare ta Nijeriya -NECO- ta fitar da sakamakon jarabawar da dalibai suka rubuta a watan Yuni/Yuli na 2019
Sakamakon jarabawar ya nuna cewa kaso 71.59% daidai da dalibai 829,787 ne suka samu cin darussa 5 ciki harda turanci da lissafi.
Kazalika kaso 89.90% daidai da dalibai 1,041,986 ne suka samu cin darussa 5, ba dole sai da turanci da lissafi ba, hakan ya nuna an samu gazawa da kaso 0.57% na bara.
Hukumar ta ce, dalibai 1,163,194 ne suka yi rajistar jarabawar tun da farko, amma 1,151,016 ne suka zauna ta, cikin su kuwa harda makafi 146.
Koken satar amsa a shekarar bana ya ninka na shekarar bara, inda a bana ake da koke-koken satar amsa har 40,630.
Mukaddashin magatakardan hukumar shirya jarabawar ta NECO Alhaji Abubakar Gana ya ce hukumar ta ware makarantu uku-uku a jihohin Katsina, Kebbi da Oyo don kara saka musu idanu ga jarabawar. Alhaji Abubakar yace ana zargin wadannan makarantun da ke wadannan jihohin uku da yin suna wajen sata da magudin jarabawa.
Sai ya kara da cewa an kama masu duba jarabawa har 18 da ake zargi da aikata mabambanta laifuk; kama daga saku-saku wajen duba jarabawa da taimakawa wajen satar amsa da hadin baki wajen rubuta satar amsa bisa allo ga dalibai.
