Hukumar shirya jarabawa ta kasa, NECO, ta fitar da sakamakon jarabawar sakandare na shekarar 2020.
Magatakardar hukumar ta NECO, Farfesa Godswill Obioma, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a shelkwatar hukumar da ke Minna, jihar Neja.
A cewarsa, kashi biyu cikin dari na daliban da suka zana jarabawar ne suka yi zarra cin darussa biyar zuwa sama a dukkan fannonin.
Magatakardar ya kuma bayyana cewa kimanin makarantu 12 ne aka soke wa sakamakon su saboda samunsu da yin magudin jarrabawa.
Ya ce daga cikin makarantun akwai guda hudu daga jihar Adamawa, biyu a jihar Kaduna, biyu a jihar Katsina, biyu a jihar Neja, daya a jihar Taraba da kuma daya a FCT.
