Shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya, farfesa Nentawe Yilwatda, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan shirin da ya bayyana na mayar da tallafin man fetur, yana mai cewa neman mulkin ƙasar bai kamata ya jefa tattalin arzikin Nijeriya cikin wani sabon haɗari ba.
Gidan talabijin na NTA News ya ruwaito Yilwatda ya bayyana wannan shawara ta Atiku a matsayin sauyin matsaya mai tayar da tambayoyi, yana cewa hakan na iya nuna rashin cikakken shirin da jam’iyyun adawa ke da shi wajen tafiyar da harkokin ƙasar idan suka samu damar karɓar mulki.
Shugaban APC ɗin ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar ƙungiyar City Boy Movement da ke Abuja, inda ya duba wasu daga cikin ayyuka da kayan aikin ƙungiyar tare da tattaunawa da shugabanninta.
Ya ce ‘yan Nijeriya sun cancanci samun fiye da alkawuran da ake yawan bayarwa a lokacin zaɓe kawai, yana mai jaddada cewa duk wata shawarar dawo da tallafin man fetur dole ne a bincike ta sosai saboda irin nauyin da kuɗin tallafin ke da shi kan tattalin arzikin ƙasar da kuma matsalolin da tsarin ya haifar a baya.
A cewarsa, APC ta sha ƙalubalantar jam’iyyun adawa cikin shekaru uku da suka gabata da su gabatar da wata bayyananniyar hanya ta daban kan manufofin gwamnatin da APC ke jagoranta, amma har yanzu ba a ga wata gamsasshiyar mafita mai ƙarfi da za ta maye gurbin waɗannan manufofi ba.
Yilwatda ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa Atiku zai fito da wannan sabon tsari ne a daidai lokacin da ya rage kusan watanni huɗu a gudanar da babban zaɓen 2027, yana neman bayyana wata manufa da za ta iya maye gurbin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ta ce sun kasance masu wahala amma wajibi ne a aiwatar da su.
Ya ce bai kamata a mayar da manufofin tattalin arziki kayan neman kuri’a ba, yana mai cewa dole ne ‘yan Nijeriya su san yadda za a samar da kuɗin da za a sake kashewa wajen tallafin man fetur da kuma ko tsarin zai dore ba tare da sake jefa gwamnati cikin matsin lambar neman kuɗaɗen da ya sa aka ɗauki matakin cire tallafin ba.
Shugaban APC na ƙasa ya nanata cewa cire tallafin man fetur mataki ne mai wahala, amma wanda yake ganin ya zama dole, yana mai cewa wajibi ne gwamnati ta ci gaba da ɗaukar matakan rage raɗaɗin tasirinsa ga jama’a, tare da faɗaɗa shirye-shiryen tallafin jin ƙai da kuma ƙarfafa ɓangarorin tattalin arziki masu samar da ayyukan yi da bunƙasa samar da kayayyakin more rayuwa a kasar.
