Home Coronavirus Nijar: Adadin masu corona ya zarta dubu daya

Nijar: Adadin masu corona ya zarta dubu daya

140
0

Yakuba Umaru Maigizawa

Adadin mutanen da suka harbu da cutar Covid-19 a Nijar sun zarta dubu daya a yanzu haka kamar yadda hukumomin lafiyar kasar suka tabbatar.

Sakamakon ranar Lahadi ma dai da gwamnatin ta fitar ya nuna cewa mutum 6 ne sabbin kamuwa aka samu a fadin kasar.

A jimilce ce dai yanzu haka mutane 1,074 aka tabbatar sun harbu da cutar cikin su 939 sun warke 67 sun hadu da ajalinsu sai ragowar 68 da suke samun kulawar likitoci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply