Home Kasashen Ketare Nijar: Alkalai sun sake tsunduma yajin aiki a karo na biyu

Nijar: Alkalai sun sake tsunduma yajin aiki a karo na biyu

89
0

Yakuba Umaru Maigizawa

Kungiyar alkalai ta kasar Nijar wato SAMAN a takaice ta sake tsunduma wani sabon yajin aiki na kwanaki uku daga ranar Litinin din nan.

Wannan dai na zama karo na biyu ke nan da kungiyar alkalan shari’ar ke shiga yajin aikin a kasa da mako biyu inda ko a ranar 26 ga watan
Disambar da ya gabata, sun gudanar da wani yajin aikin na kwanaki biyu(2).

Kungiyar na kalubalantar ministan shari’ar kasar ne a kan wata doka da suke ga ta saba ma tsarin shari’ar kasar, duk da ya ke tuni dokar ta samu amincewa daga ‘yan majalisar dokokin kasar.

Sai dai alkalan kasar, na neman shugaban kasa ya shiga lamarin inda shi kadai ne yanzu zai iya bukatar sake duba dokar kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada.

Ya zuwa yanzu dai magatakardar kungiyar na kasa Nouhou Aboubacar ya shaida ma jaridar DCL Hausa cewa gwamnati bata ce komai ba sai dai ya ce a shirye suke da su zauna a teburin tattaunawa da gwamnatin idan har ta kira su kamar yadda doka ta tanada.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply