Home Kasashen Ketare Nijar: an ceto wasu ‘yan mata 7 daga wani mai safarar mutane

Nijar: an ceto wasu ‘yan mata 7 daga wani mai safarar mutane

75
0

Yakuba Umaru Maigizawa

A ya yin wani taron manema labarai ne da suka kira, hukumomin da ke kula da yaki da safarar mutane a jihar Damagaram ta jamhuriyar Nijar suka gabatar da wasu ‘yan mata da aka ceto da aka yi yunkurin safara zuwa ketare ga ‘yan jarida

Hukumomin sun gabatar da ‘yan matan guda bakwai (7) ne da suka ce guda 4 dukkan su ‘yan shekara 14 ne, ya yin da dayar take da shekara 15 da kuma guda ‘yar shekara 18 sai babbar cikin su ‘yar shekara 21 kamar yadda Abdulayi Lawali ya bayyana a gaban manema labarai.

Abdulayi Lawalin wanda shi ne shugaban wata sabuwar cibiyar hukumar da ke kula da mutanen da suka fada tarkon masu safarar bil’adama ta birnin Damagaram, ya bayyana cewa an yi nasarar ceto wadannan ‘yan matan ne a filin jirgin sama jihar Kanon Tarayyar Najeriya inda ejan “agent” da ke kokarin safarar ta su zuwa Saudiyya ya ranta a na kare.

To sai dai bayan cabke ‘yan matan an gano cewa sun samu fasfo ne daga jihar Katsina inda nan take aka tuso keyarsu zuwa jihar ta Katsina sai kuma daga bisani aka gano ‘yan yankin Magaria ne da ke jihar Damagaram ta jamhuriyar Nijar, a nan take ba tare da wata-wata ba kuma aka miko su ga hukumomin jihar

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin ‘ya’ya mata da yaki da cin zarafin ‘ya’ya mata suka yaba da wannan nasara

Wannan dai shi ne karo na farko da wannan sabuwar cibiya da ake ga irinta ce ta farko a gabacin kasar ta karbi wasu mutanen da suka fada tarkon masu safarar bil’adamar tun bayan kaddamar da ita kusan shekara guda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply