Home Kasashen Ketare Nijar: An dakatar da rajistar masu zabe

Nijar: An dakatar da rajistar masu zabe

77
0

Yakuba Umaru Maigizawa

Hukumar zabe ta Nijar wato CENI ta sanar da dakatar da ayyukanta na rajistar masu zabe a wasu yankuna na kasar sakamakon matsalar tsaro.

Wannan mataki dai ya shafi wasu kananan hukumomi ne na jihohin Tahoua da Tillaberi masu iyaka da kasar Mali da kuma ke fuskantar barazanar ‘yan ta’adda.

Kananan hukumomin kuwa sun hada da Tillia dake jihar Tahoua sai kuma wasu guda 8 dukkan su a cikin jihar Tillaberi da suka hada da Abala, Tondikiwindi, Makalondi, Torodi, Gouroual, Diagourou, Inates, Banibangou.

Shugaban hukumar Metir Issaka Sounna ya bayyana cewa za su sake dawowa aikin rajistar yankunan idan tsaro ya daidaita.

Sai dai tuni ‘yan adawar kasar suka nuna takaicinsu dangane da wannan mataki tare da zargin hukumar na shirin tabka magudin zabe.

To sai dai ko a kwanakin baya ma wasu ‘yan ta’addar sun kai ma wata tawagar jami’an hukumar zaben hari a yankin Tillaberi inda suka hallaka wasu jami’an tsaron da ke masu rakiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply