Home Labarai Nijar: An kaddamar da fara rajistar katin zabe

Nijar: An kaddamar da fara rajistar katin zabe

73
0

Yakuba Umaru Maigizawa/Jani

Hukumar zabe ta kasar Jamhuriyar Nijar mai zaman kanta CENI ta kaddamar da fara rajistar katin zabe na zamani wato “biométrique” a jihar Agadez da ke arewacin kasar.

Za a fara amfani da wannan katin zabe na zamani ne a karon farko a zaben kasar kuma zai taimaka kwarai wajen kiyaye tabka magudin zabe.

Katin dai na zamani na kunshe ne da hoton mamallakinsa tare da zanan sawu yatsun mai shin wanda ke nuni da cewa wani ba zai yi amfani da wani ba.

Jamhuriyar Nijar dai ta bi sahun takwarorinta kasashen nahiyar Afirka da suke amfani da tsarin tun nan da wasu shekaru.

Tuni dai wasu jam’iyyun siyasa kamar su PNDS Tarayya suka fara wayar da kan magoya bayansu kan sabon tsari.

To sai a nasu bangaren, jam’iyyun adawar kasar na ci gaba da haramta aikin hukumar zaben CENI sakamakon zargin da suke na rashin sahihancin hukumar.

Sai dai ko a baya-bayan nan, sakataren gwamnatin kasar ya bayyana cewa za a tafi zaben ko da ‘yan adawa ko babu su.

Abin jira dai a gani shi ne irin abin da matakin na ‘yan adawa zai haifar idan dai har ba su janye wannan aniya tasu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply