Home Kasashen Ketare Nijar: An rufe asibiti masu zaman kansu guda 6

Nijar: An rufe asibiti masu zaman kansu guda 6

83
0

Yakuba Umaru Maigizawa, abokin aikinmu a Damagaram Nijar

 

 

A ci gaba da ziyara aiki da yake a wadansu asibitoci masu zaman kansu, ministan kiwon lafiya na jamhuriyar Nijar, dokta Idi Illiassou Mainassara ya bada umarnin rufe wasu asibitoci masu zaman kansu a birnin Yamai ciki kuwa harda daya mallakar wani ma’aikacin gwamnati.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta bayyana cewa cibiyar kiwon lafiyar ta ma’aikacin gwamnatin na nan ne cikin unguwar Banifandou da ke birnin Yamai inda kuma gwamnatin ta ce asibitin bai samu izinin yin aiki daga gwamnati a hukumance ba.

Wani asibiti a jamhuriyar Nijar

Sanarwar ta kuma ce an taka dokar da ke cewa aikin kiwonlafiya mai zaman kanshi baya haduwa da dukkan wani nau’in aikin gwamnati.

Ko baya ga wannan asibitin dai umarnin na minista ya shafi wasu asibitocin masu zaman kansu guda biyar(5) dukkansu a birnin Yamai inda ake zarginsu da gudanar da ayyukansu ba akan ka’ida ba.

A shekarar bara ma ministan ya tsaida wasu asibitoci masu zaman kansu da dama sakamakon rashin bin ka’idar aiki.

Karkashin wannan tsari dai gwamnatin ta ce za ta ci gaba da sa  ido dan ganin ta tsabtace fannin kiwan lafiyar.

 

Yakuba/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply