Home Kasashen Ketare Nijar: an yi wa Majalisar Ministoci garambawul

Nijar: an yi wa Majalisar Ministoci garambawul

63
0

 

Yakubu Maigizawa, Damagaram.

 

 

Gwamnatin kasar Nijar ta yi wa majalisar ministocinta garanbawul a ya yin wani taron majalisar ministocin da ya gudana a ranar Juma’a a babban birnin Yamai karkashin jagorancin shugaban kasa Elhaji Isufu Mahamadou.

Wannan garanbawul dai ya shafi canja ma’aikatu da kuma sabbin nade-nade a cikin majalisar da ke kunshe da sama da ministoci 40.

Ma’aikatar tsaro ta samu sabon jagora inda a ka nada Isufu Katanbe ya canji tsohon ministan tsaro Malan Kalla Mutarai, ya yin da shi kuma a ka mai da shi ministan kula da harkokin ruwa, Ma’aikatar cikin gida ta samu sabon karamin minista a cikin wannan garanbawul.

Sai dai abin da ya fi daukar hankali a cikin wannan garanbawul shi ne na sake bayyanar sunan tsohon ministan kudi Malan Hasumi Masa’udu da a ka tsige daga mukaminsa da rana tsaka a watannin da suka gabata a matsayin ministan kasa a fadar gwamnati.

Abin jira a gani dai shi ne irin tasirin da wannan garanbawul ka iya yi a fannin tafiyar gwamnatin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply