Home Kasashen Ketare Nijar da Mali sun yi tir da kisan Turawa 6

Nijar da Mali sun yi tir da kisan Turawa 6

148
1

A ranar Lahadi nan ne wasu mahara bisa babura dauke da makamai suka kai hari kan wasu Turawa ‘yan kasar Faransa da ke yawon bude ido a yankin Kouré da ke jihar Tillaberie kan iyaka da kasar Burkina Faso.

‘Yan ta’addar sun hallaka mutanen 8 ne da suka hada da ‘yan kasar Faransa 6 da ke yawon bude ido tare da mutum biyu ‘yan Nijar da suka hada da direban motar sai kuma wanda ke musu jagora wajen gwada musu ababe kafin daga bisani su cinnawa motar wuta.

Tuni dai gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ba da umurnin yin samame a yankin, don farautar wadanda suka aikata wannan kisa da tuni shugabannin kasashen Nijar da Mali suka yi tir da Allah wadai da shi tare da mika sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Faransa da kuma dangin sauran ‘yan Nijar din da suka rasa ransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply