Yacouba Damagaram/Banye
A yau ne ake kawo ƙarshen wani taron ƙwararru da masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimin boko a ƙasar Nijar, wanda jihar Tahoua ke karɓar baƙuncin sa a bana ƙarƙashin jagorancin ministan ilimin ƙananan makarantun boko.
Taron dai na kwanaki biyu da aka buɗe jiya Litinin zai bada damar a ƙaddamar da wasu gyare gyare a cikin tsarin koyarwar ƙasar.
Wannan taro da ake gudanar da shi duk shekara, yana ƙoƙarin lalubo hanyoyin bunƙasa ilimi a ƙasar, ta hanyar samun shawarwari tsakanin ƙwararru da kuma masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi.
