Home Kasashen Ketare Nijar: kungiyar dalibai ta kalubalanci korar da aka yi wa dalibai sama...

Nijar: kungiyar dalibai ta kalubalanci korar da aka yi wa dalibai sama da 20,000

81
0

Yakubu Maigizawa, Damagaram

A yau ne a fadin kasar jamhuriyar Nijar aka koma karatu a fannin makarantun share fagen shiga Jami’a.
A jihar Damagaram dai mukaddashin Gwamnan jiha ne Harou Maman tare da rakiyar magajin gari da hukumomin ilimin jihar suka kaddamar da fara karatun bana a cikin makarantar CES Barma Moustapha da ke zama makarantar farko a fannin Sakandare a Damagaram.


Tuni dai magatakardar Gwamnan jihar ya mika kayayyenkin karatun ga wasu dalibai a gaban ‘yan jaridu. Sai dai wannan komawa karatu na zuwa ne a dai-dai lokacin da malaman makarantun ke kokawa wajen rashin samun albashinsu na watan da ya gabata.

Ana su bangaren daliban makarantun sakandaran sun kira wani taron manema labarai karkashin jagorancin magatakardar kungiyar tasu ta jihar Damagaram Habu Mummuni a ranar asabar din da ta gabata inda suka kalubalanci hukumomin ilimin akan abubuwa da dama ciki kuwa har da batun korar wasu dalibai kimanin dubu ashirin da hudu da dari takwas (24800) a cikin jihar Damagaram kadai a shekarar karatun bara sakamakon rashin samun makin da zai basu damar maimaita ajin da suke ko kuma ketare shi.


Abin jira dai a gani shi ne yadda shekarar karatun banar za ta kasance ganin irin yadda ta fara da haka, koda yake malaman da daliban sun amsa kiran magabata na komawa karatun a yau litinin 16.09.2019

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply