Home Kasashen Ketare Nijar: Kungiyar ECOWAS ta gudanar da taron gaggawa saboda siyasar Guinée Bissau

Nijar: Kungiyar ECOWAS ta gudanar da taron gaggawa saboda siyasar Guinée Bissau

84
0

A ranar Juma’ar nan ne, shugaban kasar Nijar Alhaji Isufu Mahamadu wanda kuma shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ya jagoranci wani taron gaggawa a birnin Yamai.

 

Wannan taron gaggawa dai da kungiyar mai kunshe da kasashe 15 daga yammacin Afirka ta kira, ta kira shi ne domin tattaunawa kan rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Guinée Bissau.

 

Kasar Guinée Bissau dai wadda ta mamba ce a kungiyar, ta tsinci kanta a cikin rikicin siyasa da ya kai har ga shugaban kasar José Mario Valse ya rushe majalisar gwamnatinsa tun daga kan Firaiministan tare da nada wani sabo da wasu mambobin majalisar.

 

Sai  dai wannan mataki shi ne ya janyo fushin kungiyar ECOWAS inda a wurin taron nata na Nijar ta bukaci sabbin mambobin gwamnatin da su yi murabus nan take.

Hotan wasu daga cikin shugabannin Afirka Ta Yamma da suka halarci taron ECOWAS na gaggawa a Nijar

Taron na yini guda na birnin Yamai ya karkare ne da fito da wata sanarwa da aka wakilta wasu shugabannin kasashen kungiyar su isa kasar ta Guinée Bissau domin mika ta ga shugaban kasar.

 

A ranar 24 ga wannan watan na Nuwamba ne dai aka tsara kasar za ta gudanar da zabe.

 

 

A daya bangare kuma taron ya tabo batun matakin gwamnatin Nijeriya na rufe iyakokinta da kasashe makwabtanta inda aka bayyana ranar 7 ga watan gobe a matsayin ranar da wasu shugabannin kasashe za su hallara a Abuja don lalubo mafita kan wannan batu.

 

Abin jira dai a gani shi ne tasirin da wannan taron gaggawa zai yi wajen samun mafita ga wadannan batutuwa da taron ya tattauna a kai.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply