Home Labarai Nijar: majalisa ta amince gwamnati ta ciyo bashin kudi Bilyan 100 na...

Nijar: majalisa ta amince gwamnati ta ciyo bashin kudi Bilyan 100 na CFA

58
0

Yakuba Umaru Maigizawa/Jani

A ranar Talatar da ta gabata, ‘yan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, a ci gaba da zaman da suke na biyu(2) a cikin wannan shekara ta 2019 da aka bude tun ranar 25 ga watan Satumba, suka amince da bukatar gwamnati na karbo bashin kudi bilyan 100 na CFA.

Daga cikin wannan bashi kuwa, za a zuba kimanin bilyan 71 a bangaran babban aikin madatsar ruwa nan ta “Kandadji” da ke cikin jihar Tillabery don ci gaba da aikin da ake sa ran kamallawa a shekarar 2024.

Jim kadan bayan kammala jefa kuri’ar amincewar ne dai, mukaddashin gwamnati, minista, kuma darakta a fadar shugaban kasa Ouhoumoudou Mahamadou ya yi godiya ga ‘yan majalisar da suka nuna amincewarsu ga bukatar ta gwamnati.

Ministan ya yi karin bayani kan muhimmancin madatsar ruwan ta Kandadji inda ya ce “aiki ne mai matukar muhimmanci da ke cikin manya-manyan aikin da gwamnati ta sa a gaba cikin tsarin nan na farfado da kasar da ake cema “Renaissance”.

Ouhoumoudou Mahamadou ya kara da cewa tuni dai a karshen watan Satumbar da ya gabata, aikin ya kai kaso 12 cikin 100, ya kuma kara da cewa da zarar an kammala gina wannan madatsar ruwa ta Kandadji za ta ba da damar samun karfin mégawatt 130 na wutar lantarki, da kuma samun damar noma tan dubu dari da saba’in(170 000) na shinkafa, sai kuma wani tan din dubu goma sha daya (11.000) na masara.

A yayin wannan zama dai ‘yan majalisar sun sa hannu kan karin wasu dokoki biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply