Home Kasashen Ketare Nijar: Malaman Jami’o’i Sun Tsunduma Yajin Aiki

Nijar: Malaman Jami’o’i Sun Tsunduma Yajin Aiki

67
0

Yakuba Umaru Maigizawa/Jani

A ranar Alhamis din nan ne malaman Jami’o’in babban birnin Yamai da Tahoua suka Shiga wani yajin aiki na sai baba ta gani.

Wannan kuwa sakamakon rashin samun albashinsu na watan Satumbar da ya gaba.

Malaman dai sun yi ikirarin ba za su koma bakin aikin ba har sai an biya su albashinsu kamar yadda yarjejeniyarsu da gwamnati ta tanada mai cewa da zaran wata ya kai kwana takwas(8) suna da ‘yancin ajiye aiki har sai an biya su.

To sai dai wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake cika wata guda da komawa bakin karatun bayan kammala dogon hutun shekarar karatun bara.

Abin jira dai a gani shi ne matakin da zai biyo baya daga sauran takwarorinsu na sauran Jami’o’in da ba su Shiga cikin wannan yajin aiki ba .

Tuni dai iyayen wasu dalibai suka fara kokawa da wannan mataki inda suke kira ga gwamnatin da ta yi kokari ta biya malaman hakkokinsu don ganin karatun ya tafi a dai dai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply