Home Kasashen Ketare Nijar : Ministan kiwon lafiya ya bayyana a gaban majalisar dokoki

Nijar : Ministan kiwon lafiya ya bayyana a gaban majalisar dokoki

83
0

 

 

A karshen makon da ya gabata ‘yan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar suka mika takardar bukatar sauraran ministan kiwon lafiya na kasar don ya bayyana a gabansu.

‘Yan majalisar dokokin sun bukaci ministan ya yi musu karin haske dangane da irin matakin da gwamnatin Nijar ke dauka akan inganta asibitocin gwamnatin da ke fama da dumbun matsaloli musamman a yankunan karkara.

To sai dai ministan Dakta Idi Illiyasu Mainasara ya bayyana cewa a matsayin su na gwamnati suna yin iya kokarinsu wajen inganta fannin kiwon lafiyar’yan kasar.

 

Minista Mainasara ya ce kimanin miliyan 200 na CFA gwamnati ke zubawa a kowane mako guda cikin tsarin nan na yima yara daga jinjirai zuwa ‘yan shekaru 5 magani kyauta gami da kula da mata masu juna biyu har ya zuwa haihuwarsu.

To sai dai ‘yan majalisar dokokin sun kalubaci wannan magana ta minista inda suke bayyana cewa ai samsam abin da suke gani a zahiri ko kadan bai yi dai dai da abin da ministan ya fada ba.

Honorable Abdu Magawata dan majalisa a karkashin tutar jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulkin Nijar ya aje takardar bukatar bayyanar ministan a gaban majalisar.

Abin jira dai a gani shi ne matakin da gwamnati za ta dauka na kara inganta kiwon lafiyar ‘yan kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply