Home Kasashen Ketare Nijar: Ministocin Afirka 125 sun hadu don nema wa kasashensu zaman lafiya

Nijar: Ministocin Afirka 125 sun hadu don nema wa kasashensu zaman lafiya

78
0

Babban zauran taron Palais des congrès na birnin Yamai ya karbi bakuncin mutane sama da dubu biyu wadanda suka hadu don lalubo hanyar da kasashe musamman na Afirka Ta Yamma za su sami saukin kalubalen tsaro da suke fuskanta.

Matsalar tsaro dai ta addabi kasashen Sahel irinsu Nijar da Mali da Burkina Faso. Ga kuma matsalar Boko Haram wace ta yi kaurin-suna a wurin hana Nijeriya da wasu makwabtanta zaman lafiya. Sai kuma ga shi shugabanni da suka hada da Shugaba Isufu Mahamadu na jamhuriyar Nijar da wasu tsofaffin shugabannin  Afirka da masu ci yanzo da shugabannin majalisun dokoki da kimanin ministoci 125 da sarakunan gargajiya sama da 300 da wakillan addinai da na ‘yan kungiyoyin farar hula kimanin 750 sun taru a Yamai babban birnin kasar Nijar don magance irin wadannan kalubalen tsaron.

Mahalarta taron na Yamai, Jumhoriyar Nijar

Taron da ke zama karo na uku dai kungiyar Fédération pour la Paix Universelle FPU ce ta shirya shi kuma ya samu halartar shugaban wannan kungiya Dakta Hak Jan Moon

Za’a kammala taron a ranar asabar mai zuwa 30 ga watan Nuwambar nan. A na sa ran  a karshe za’a fito da sanarwar karshe da za ta maida hankali kan lalubo mafita dangane da samun dawwamamman zaman lafiya.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply