Home Kasashen Ketare Nijar: Sojoji 12 sun mutu sakamakon harin ‘yan bindiga

Nijar: Sojoji 12 sun mutu sakamakon harin ‘yan bindiga

86
0

Yakuba Umaru Maigizawa

A wata sanarwa da ta fitar ma’aikar tsaron Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar sojojin kasar 12 ya yin da wasu 8 suka samu jikkata sakamakon wani hari a yankin jihar Diffa.

Wannan hari dai an kai shi ne a daren Talata 29 ga wannan wata wayewar Laraba a cikin wani barikin sojin kasar da ke Blabrine yankin da ke da nisan kilomita 45 da garin N’guigmi.

Sai dai wata majiya da ba ta gwamnati ba, na nuni da cewa ko baya ga asarar rayukan, ‘yan bindigar da ake kyautata zatan ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun cinna wa motoci da wasu makaman sojojin wuta yayin da suka yi awon gaba da wasu duk da yake cewa wata majiyar na cewa an kwato su.

Yankin Diffa dai da ke da iyaka da kasashen Tchadi da Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro, na cikin dokar ta baci ne tun wasu shekaru da fara fuskantar hare-haren na ‘yan kungiyar Boko Haram.

To sai dai duk da wannan doka, yankin da ke kudu maso gabashin kasar na ci gaba da fuskantar hare-haren da ma yin garkuwa da mutane inda ko a baya-bayan nan wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da magajin garin Kabalewa da matarsa wadanda har ya zuwa yanzu ba a sako su ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply