Hukumomin kiwan lafiya na jamhuriyar Nijar sun bi sahun wasu takwarorinsu na fadin duniya wajen daukan matakin rigakafin bular cutar coronavirus da ta bulla a kasar China a baya-bayan nan. Cutar na ci gaba da bazuwa a fadin duniya.
A wata sanarwa ce da aka fitar a yayin zaman Majalisar Ministoci gwamnatin ta wallafa daukan matakin da ya maida hankali musamman a filin jirgin birnin Yamai.
Hukumomin sun bayyana cewa sun dauki matakin karfafa sa idon masu shiga da fice a filin jirgin sama tare da wayar da kan ma’aikatan filin jirgin a matakin dakile duk wata barazana ta bullar cutar da ke ci gaba da bayyana a wasu kasashen duniya.
