Home Labarai Nijar: Tirmitsitsin amsar tallafi ya yi silar kashe mutum 20 da jikkata...

Nijar: Tirmitsitsin amsar tallafi ya yi silar kashe mutum 20 da jikkata wasu 12 a Diffa

56
0

Yakuba Umaru Maigizawa

Akalla mutane 20 ne suka hadu da ajalinsu tare da jikkatar wasu 12 a jihar Diffa da ke jamhuriyar Nijar sakamakon wani tirmutsitsi.

Akasari wadanda lamarin ya ritsa da su dai yara ne da mata da sukaje karbar kayan tallafi da gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum ya kaiwa ‘yan gudun hijira da suka fito daga jihar sa.

Lamarin ya faru ne a gidan raya al’adun matasa (MJC) da ke birnin Diffa a yau Litinin, lokacin da mutanen suka yi cincirindo wajen karbar maitakon.

Rahotanni na cewa dai gwamnan ya raba taimakon Naira 5,000 da turmin atanfa ga ko wace mace, sai buhun shinkafa da mai galan daya ga ko wane magidanci.

A yanzu haka dai wadanda suka jikkatar suna babbar asibitin birnin Diffa inda gwamnan Diffa tare da shugaban majalisar mashawartan jihar suka ziyarci asibitin domin duba halin da suke ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply