Home Kasashen Ketare Nijar: Za a hana taron ibadoji don guje wa cutar Corona Virus

Nijar: Za a hana taron ibadoji don guje wa cutar Corona Virus

96
0

Yakuba Umaru Maigizawa

Shugaban kasar Nijar Isufu Mahamadu ya gabatar da wani jawabi na musamman ga ‘yan kasar domin bayyana sabbin matakan da gwamnati ta dauka na rigakafin bullar cutar coronavirus.

A cikin jawabin da aka watsa kai tsaye ta kafar talabajin ta kasar, shugaba Isufu Mahamadu ya bayyana cewa ganin irin ci gaba da yaduwa da annobar cutar ke yi a duniya da ma kasashen Afirka ya zama dole gwamnati ta kara karfafa matakan rigakafin.

Matakan kuwa sun hada da:

Rufe filayen jirage na kasa da kasa na jihohin Damagaram da babban birnin Yamai na tsawon sati biyu daga 12 daren 19 ga watan Maris.

Rufe illahirin iyakokin kasa na kasar da sauran kasashe na tsawon mako biyu da zai fara daga 12 daren 19 ga watan Maris kin nan.

Sasantawa tsakanin gwamnati da jagororin addinai dan duba yadda za a tsaida halartar wuraren ibada.

Rufe illahirin makarantun kasar tun daga matakin firamari har zuwa na matakin jami’o’i na tsawon mako biyu daga karfe 12 na daren 20 ga watan Maris.

Rufe dukkan wasu mashaya da wuraren shakatawa da ma gidajen kallo(cinéma) daga karfe 12 daren 18 ga watan nan

Haramcin taron al’umma da ya wuce mutune 50, wannan kuwa ya shafi taron aure ko suna da ma dukkan wasu shagulgula a duk fadin kasar.

Gwamnatin ta kuma bukaci a karfafa tsabta a wuraren kasuwa, wajen saida abinci, ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.

Gwamnatin kuma ta bukaci mutane su rika sa tazara ta kimanin mita 1 a tsakanin su a wuraren abinci da ma ma’aikatu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply