Home Kasashen Ketare Nijar@61: Shugaba Isufu zai bude gidauniyar kula da ‘ya’yan sojojin da suka...

Nijar@61: Shugaba Isufu zai bude gidauniyar kula da ‘ya’yan sojojin da suka mutu a fagen daga

79
0

Shugaba Issoufou Mahamadou ya tabo batutuwa daban daban da suka hada fannnin tsaro a cijin jawabinsa ga yan kasar daren ranar Larabar nan.

Ya ce wannan hari na baya bayan nan da aka kai wa sojojin kasar, ya yi alkawalin cewa gwamnati za ta dauki matakin bude wata gidauniya ta musamman dan tallafa ma diyan sojojin da suka rasa ransu a wajen kare kasar.

Shugaban ya bayyana cewa za’a sanya ma wani dandalin shakatawa na cikin birnin Yamai sunan Lieutenant colonel Hassane Anoutab shugaban bataliyar sojojin na Inates da suka rasa ransu a filin daga da ci gaba da tunawa da irin jarumtar da ya yi.

A dazu ne dai za’a gudanar da faretin sojoji a gaban shugaban kasar a jihar Tillabery da ke karbar bakuncin sallar a bana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply