Gwamnatin Nijeriya ta ba da hutun ranar ‘yancin kai Alhamis 1 ga Oktoba, 2020.
Ministan cikin gida Rauf Aregbesola da ya ayyana wannan rana, ya taya ‘yan Nijeriya murnar cikar Nijeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda daga babban sakatare na ma’aikatar Georgina Ehuriah, mai taken “Murnar Ranar ‘Yancin Kan Nijeriya Na Shekaru 60”.
