Nijeriya ta samu matsayi mafi muni a jerin ƙasashen da suka fi cin hanci a duniya inda take matsayi na 149 da maki 25 cikin 100, a rahoton ƙungiyar Transparency International na shekarar 2020.
A rahoton shekarar 2019 da ƙungiyar Transparency International ta fitar Nijeriya na matsayi na 146 cikin ƙasashe 180 da maki 26 cikin 100.
A cewar rahoton Nijeriya ita ce ƙasa ta biyu da aka fi cin hanci a yankin Afirka ta Yamma, bayan Guinea-Bissau yayin da take matsayi na 13 a Nahiyar Afrika.
