Home Labarai Nijeriya ce kasar da ta fi yawan matalauta a duniya – El-Rufai

Nijeriya ce kasar da ta fi yawan matalauta a duniya – El-Rufai

21
0

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce Nijeriya ce ta fi kowace kasa yawan matalauta a fadin duniya.

El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a lokacin da aka kaddamar da hukumar kula da jin dadin jama’a kare a Kaduna.

El Rufa’i yace gwamnati ta kafa wannan hukuma domin ganin an isar da duk wani tallafi a inda ya kamata domin rage wa mutane bakin talaucin da ya yi musu katutu.

El Rufa’i yace sai Nijeriya ta jingine tsarin bayar da tallafin masu karamin karfi ya biyo ta hannun attajirai, sannan zata magance matsalar talauci.

DCL Hausa ta rawaito cewa, Gwamnan ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hali, da su rika bada tallafi kai tsaye ga mabukata ba tare da an yi ‘yan biye-biye ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply