DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeBabban Labari Nijeriya ce ta biyu a ƙasashe mafi tsawon hanyoyin mota a Afrika—...

Nijeriya ce ta biyu a ƙasashe mafi tsawon hanyoyin mota a Afrika— Rahoto

Nijeriya ta zama ƙasa ta biyu a Afirka mai mafi tsawon hanyoyin mota, inda jimillar hanyoyin mota da ake amfani da su a ƙasar ta kai kimanin kilomita 195,000, bisa bayanan shekarar 2026 na Global Firepower.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Nijeriya ta zo ta biyu a Afirka, yayin da take matsayi na 28 a duniya wajen tsawon hanyoyin mota.

Kasar Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a nahiyar, inda take da kimanin kilomita 750,000 na hanyoyin mota.

Habasha ce ta zo ta uku da kilomita 180,000, yayin da Kenya ke matsayi na huɗu da kilomita 161,452.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ce ta biyo baya da kilomita 152,373, sai Tanzania mai kilomita 145,203.

Mali ta zo ta bakwai da kilomita 139,107, yayin da Aljeriya ke matsayi na takwas da kilomita 112,696.

Zimbabwe ce ta tara da tsawon kilomita 97,267, sannan Sudan ta Kudu ta kasance ta goma da kilomita 90,200.

Rahoton ya bayyana cewa Amurka ce ke da mafi tsawon hanyar mota, da kilomita 6,586,610, sai Indiya da kilomita 6,371,847, sannan China mai kusan kilomita miliyan 5.2.

Brazil ce ke matsayi na huɗu a duniya da kusan kilomita miliyan biyu, yayin da Rasha ke matsayi na biyar da kilomita 1,283,387.

Rahoton ya ce wannan ƙididdiga tana auna tsawon hanyoyin mota da ake iya amfani da su, ba wai ingancin hanyoyin, yanayinsu ko adadin hanyoyin da aka shimfiɗa da kwalta ba.

Saboda haka, kasancewar Nijeriya ta zo ta biyu ba yana nufin ita ce ta biyu wajen ingancin hanyoyi a Afirka ba; matsayi ne da ya dogara ne kawai da jimillar tsawon hanyoyin mota.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata