Nijeriya da Saudiyya sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwar soji da faɗaɗa hulɗa a fannonin tsaro da kare ƙasa, domin inganta ƙwarewar jami’an tsaro da tunkarar matsalolin tsaro da suka shafi ƙasashen biyu.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar ban-girma da jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, ya kai hedikwatar tsaron Nijeriya a ranar Laraba.
A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ziyarar ta ba ƙasashen biyu damar sake tabbatar da aniyarsu ta zurfafa dangantakar soji-da-soji, tare da gano wasu ƙarin fannoni da za su amfanar da ƙasashen biyu.
Da yake karɓar jakadan, babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede ya yi maraba da ziyarar, tare da bayyana godiyar Nijeriya ga masarautar Saudiyya bisa kyakkyawar dangantakar da ta daɗe tana tsakanin ƙasashen biyu.
Janar Oluyede ya jaddada muhimmancin ci gaba da faɗaɗa hanyoyin haɗin gwiwa da ke akwai, musamman a fannonin da za su ƙara ƙwarewar ƙwararru da ingancin ayyukan rundunar sojin Nijeriya.
Ya ce ƙarfafa irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen samar da ƙarin ƙwarewa da dabarun da jami’an tsaron Nijeriya za su yi amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
A nasa ɓangaren, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, ya bayyana aniyar ƙasarsa na ƙara ƙarfafa dangantakarta da Nijeriya, yana mai bayyana Nijeriya a matsayin “muhimmiyar abokiyar hulɗa a Afirka.”
Ambasadan ya kuma tabbatar da cewa Saudiyya a shirye take ta ƙara kusantar Nijeriya, musamman wajen haɗin gwiwar tsaro da harkokin soja, domin amfanin ƙasashen biyu.
Kasashen biyu sun amince cewa ƙarfafa dangantakar hukumomi da ƙwarewar sojojin ƙasashen biyu zai taimaka wajen inganta haɗin gwiwa wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka zama ruwan dare.
Janar Oluyede ya kuma gode wa gwamnatin Saudiyya bisa ci gaba da nuna kyakkyawar niyya ga Nijeriya, yana mai fatan tattaunawar da aka gudanar za ta haifar da haɗin gwiwa.
Hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce ganawar ta nuna ƙudurin Nijeriya da Saudiyya na ƙara ƙarfafa dangantakarsu da kuma ciyar da muradunsu na bai ɗaya gaba, musamman wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali.
