Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola yace gwamnatin Nijeriya na bukatar kudade sama da naira tiriliyon 6 da za su taimaka mata wajen kammala ayyukan hanyoyin da take kan yi da yawansu ya kai 711.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke kare kasafin kudin ma’aikatarsa a gaban kwamitin majalisar dattawa a Abuja.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar da ya ke jagoranta za ta yi amfani da kaso 47 cikin 100 na sama da naira tiriliyon 13 da ta kasafta.
