Home Labarai Nijeriya na kashe ₦5bn duk wata wajen kula da ƴan gudun hijira

Nijeriya na kashe ₦5bn duk wata wajen kula da ƴan gudun hijira

175
0

Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan ayyuka na musamman, Sanata Yusuf A. Yusuf, ya ce gwamnatin tarayya na kashe Naira Biliyan ₦5bn ko wane wata domin kula da ƴan gudun hijira a Arewa maso Gabas.

Yusuf ya faɗi haka ne lokacin da yake yi wa ƴan jarida jawabi a Abuja kan abubuwan da kwamitin ya gano a ziyarar gani da ido da ya kar a sansanonin ƴan gudun hijira daban daban na yankin.

Ɗan majalisar ya ce dole ne gwamnatin ta kawo ƙarshen matsalolin ƴan gudun hijira domin babu wadatar kuɗin da za a riƙa kashewa maƙudai kan ƴan gudun hijirar.

A don haka ya buƙaci jami’an tsaro su zage dantse wajen yaƙi da ƴan ta’adda domin ba mutane damar komawa garuruwansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply