Mininstan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono ya ce, gwamnatin Nijeriya ta kashe kimanin Dala biliyan shida wajen shigo da alkama daga kasashen waje daga shekarar 2016 zuwa watan Yulin 2020.
Ministan ya bayyana cewa kididdigar da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar ta tabbatar da cewa ana samar da alkama kimanin tan 420,000 a cikin gida alhali bukatar da ake da ita ta kai akalla tan miliyan 5.26.
A takaice dai ana faduwa da kusan tan miliyan 4.5 da ake samu, don haka akwai bukatar saka hannun jari mai yawan gaske a bangaren noman alkama domin bunkasa noman.
