[cmsmasters_row data_shortcode_id=”weqlgr2zj” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”76a2fa5e3a” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”fdqwa3bmp” animation_delay=”0″]
Shugaban babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya ce Nijeriya na kashe makudan kudade a kowace shekara da suka kai Dala bilyan 1.2 wajen shigowa da kifi a kasar.
Godwin Emefiele ya bayyana haka ga gwamnonin wadansu jihohi da kafafen watsa labarai a wata ganawa ta musamman da suka yi a Abuja kan irin nasarorin da aka samu a harkar noma da bunkasa tattalin arziki. Ya bayyana cewa a yanzu haka Nijeriya na samar da kifi tan 800,000, alhalin bukatar kifin ta kai tan milyan 2.7. Wannan ya nuna akwai gibin tan milyan 1.9 ke nan.

Emefiele ya ce babban kudurin babban bankin Nijeriya shi ne saka gwamnonin dumu-dumu cikin harkar domin bunkasa kiwon kifi tare da kawar da shigo da kifi da a ke yi a kasar. A cewarshi, wannan wata dama ce da za ta kara tattalin arzikin jihohin ta hanyar jan hankalin masu sana’ar.
[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]
