Home Noma da Kiwo Nijeriya na son daina yin odar sukari daga ketare

Nijeriya na son daina yin odar sukari daga ketare

86
0

Abdullahi Garba Jani

 

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta rika ‘tsimin’ Dala milyan 56 ($56 Million ) idan ta takaita shigo da sukari a kasar ta. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da take hankoron samar da tan milyan daya da dubu dari bakwai na sukari daga cikin kasar.

 

Ministan ciniki, masana’antu da zuba jari na kasar Mr Otumba Adeniyi Adebayo ya furta hakan a Abuja a lokacin da ya ke karin haske ga mahukuntan cibiyar bunkasa samar da sukari ta Nijeriya. Ya lashi takobin cewa gwamnatin Nijeriya za ta ba da goyon baya da tallafi ga masu zuba jari a masana’antun sarrafa sukari na kasar don samar da shi a wadace cikin kasar.

 

Sai ya fada wa mahukuntan cibiyar irin kwazon gwamnatin kasar na ganin ta yi aiki kafada-da-kafada da masu ruwa da tsaki don shawo kan kalubalen da suke ci wa sashen tuwo a kwarya a halin da ake ciki.

 

Hotan wata gonar rake. Ana dai samar da sukari galibi daga rake

Mr Otumba Adebayo ya ce gwamnatin kasar ta yi aiki tukuru wajen inganta aikin gona, inda ministan ya bugi kirjin cewa nan ba da jimawa ba Nijeriya za ta zama tamkar kasashe irinsu Brazil da Mauritius wajen samar da sukari mai yawa da inganci.

 

Tun da farko shugaban cibiyar Dr. Lateef Busari, ya zayyano irin nasarorin da gwamnatin kasar ta samu a sashen inganta ma’aikatu da suka hada da samar da ayyukan yi. Ya ci gaba yana cewa akwai tsarin samar da ayyukan yi har 114,000 da kuma samar da tan milyan daya da dubu dari bakwai na sukari a duk shekara.

 

Dr Busari ya ce yin hakan zai rage shigo da sukarin daga kasashen waje sannan a kara adana wasu kudi har Dala milyan 56.

 

 

 

Vanguard:       Jani/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply