Home Coronavirus Nijeriya ta bude filayen jiragen saman ta

Nijeriya ta bude filayen jiragen saman ta

132
0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta bude dukkanin filayen sauka da tashi na jiragen sama, ciki hada masu zaman kansu da ma kananan filaye domin ci gaba da jigila.

Ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika ne ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabinsa a taron da kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan yaki da annobar corona ya yi a Abuja.

Hadi Sirika ya ce akwai filayen jiragen sama goma sha hudu da suka dawo aiki tun watan Yulin da ya gabata, biyo bayan kwashe watanni kusan biyar a rufe, bisa dalilin barkewar annobar corona a kasar nan.

Ya kuma ce an bude 2 daga cikin filayen jiragen sama da suka hada da babban filin jirgi na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma babban filin jirgin sama na Murtala Mohammad na jihar Legas.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply