Yanzu haka bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 31.01 a karshen watan Yunin da ya shude kamar yadda hukumar kula da ciyo bashi ta kasa ta sanar.
Hakan na nufin, a cikin shekaru 5, shugaba Buhari ya ciyo bashin da ya kai Naira tiriliyan 18.89 ga Nijeriya.
A karshen shekarar 2015, wata daya kafin gwamnatin Buhari ta hau, ana bin Nijeriya bashin Naira tiriliyan 12.12.
Jaridar Punch ta rawaito cewa ya zuwa yanzu bashin ya kai kaso 155.86% a cikin shekaru 5.
