Ministan wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman ya ce babu wani ɗan Nijeriyan da zai ce ba a samu canji a bangaren wuta ba karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
A hirar da ya yi da BBC Hausa, Saleh Mamman ya ce kashi 80 zuwa 90 na masu samun wutar lantarki za su tabbatar an samu canji na wutan lantarki.
Ya ce gaba daya Najeriya an samu karin wutar lantarki karkashin gwamnatin Buhari.
Ya kara da cewa babu gari ko anguwar da za ta ce ta kwana daya ba a kawo wuta ba sai da idan wani abu ya lalace.
