Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce ta kashe Naira Biliyan ₦30.5 wajen yaƙi da cutar Covid-19 tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin bana.
Babban akantan ƙasar Ahmed Idris wanda ya bayyana haka, ya ce kuɗin sun kai kashi 84% na yawan kuɗaɗen gudunmuwar da gwamnatin ta samu na Naira Biliyan ₦36.3 daga masu bada gudunmuwa.
Idris wanda ya bayyana haka a matsayin amsa ga buƙatar neman bayanan yadda aka kashe kuɗin da ƙungiyar yaƙi da cin hanci ta SERAP ta nema, ya ce har yanzu akwai sauran ₦5.9bn daga cikin kuɗin.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, mataimakin babban Daraktan SERAP Kolawole Oludare, ya ce babban Akantan, ya bayyana masu cewa kwamitin shugaban ƙasa kan yaƙi da cutar, ya kashe ₦22bn yayin da jihohi 36 na ƙasar suka kashe ₦7bn.
Ya ƙara da cewa rundunar sojin sama ta kashe Naira miliyan ₦877 wajen jigilar kayan yaƙi da cutar yayin da rundunar ƴan sanda ta kashe Naira miliyan 500 wajen ba kayan kariya sanna kuma aka kashe ₦17,865.09 a matsayin kuɗin cajin banki.
