Home Addini Nijeriya ta samu kujerun aikin Hajji dubu 95,000 a Hajjin 2020

Nijeriya ta samu kujerun aikin Hajji dubu 95,000 a Hajjin 2020

81
0

Abdullahi Garba Jani

Hukumar kula da aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON ta ce kasar Saudiyya ta sake ba ta adadin yawan kujerun aikin Hajjin da ta samu a 2019, kimanin dubu 95,000 a aikin Hajjin 2020.

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin wata takarda da ta fito daga mai magana da yawun hukumar Hajiya Fatima Usara a Abuja.

Usara ta ce an cimma matsayar sake ba Nijeriya yawan wadannan kujerun ne a cikin wata yarjejeniyar fahimta da aka rattaba hannu tsakanin karamin ministan harkokin waje Alhaji Zubairu Dada da kuma ministan kula da aikin Hajji da Umrah na kasar Saudiyya Saleh Benten.

Ta ce a ranar 5 ga watan Disamba ne aka saka hannu kan yarjejeniyar a wani bangare na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2020.

Fatima Usara, ta ce gwamnatin tarayya ta mika sakon godiya ga sarkin Makka Salman Bin Abdul’aziz da ya sa aka biya diyya ga iyalai 5 na wadanda suka rasa rayukan a ya yin aikin Hajjin shekarar 2015 lokacin da kugiyar ta fadowa mahajjata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply