Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Nijeriya ta shirya fara inshorar haɗarin motoci ta ECOWAS

Nijeriya ta shirya fara inshorar haɗarin motoci ta ECOWAS

34
0

Gwamnatin Tarayya ta shirya aiwatar da inshorar da zai tabbatar da biyan diyya ga wadanda hatsarin mota ya ruwa da su a kasashen yammacin Afirka na ECOWAS.

Minastar kudi da kasafi Zainab Ahmed ta bayyana haka a lokacin kaddamar da shugabannin hukumar da za ta kula da tsarin inshorar wadda Ganiyu Musa zai jagoranta, wanda ya gudana a Abuja.

Minister ta yi bayanin cewa kaddamar da shirin inshorar, zai taimaka wa kokarin kafa tsarin kasuwanci kyauta tsakanin kasashen na ECOWAS.

Ministar wadda ta samu wakilcin kwamishinan inshore daga hukumar Inshora ta kasa Sunday Thomas, ta yi maraba da tsarin, wanda zai bada damar hada-hadar kasuwanci da bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen yammacin Afirka.

Ta ce akwai kalubale da ya kamata a magance, a daidia lokacin da shugaban hukumar inshorar zai fara aikinsa, wadanda suka hada da rashin girmama yarjejeniyar da kasashen yankin ke shiga, jinkiri wajen biyan wadanda hadurran suka rutsa da su da kuma rashin samar da isassun kudi ga hukumar da dai sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply