Home Sabon Labari Nijeriya za ta karbi bakuncin gasar ƙwallon raga ta Afirka

Nijeriya za ta karbi bakuncin gasar ƙwallon raga ta Afirka

91
0

Ma’aikatar kula da harkokin wasanni da matasa ta kasa ta amince da rokon da ƙungiyar wasan kwallon raga ta kasa ta yi na son daukar nauyin wasan raga ta Mata ƴan kasa da shekaru 18 na Afrika.

Jami’in yada labarai na kungiyar Kahinde Lamidi ne ya bayyana hakan a jiya cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa gasar cin kofin ta mata za ta gudana ne a babban filin wasa na kasa dake Abuja daga 29 ga watan Janairu zuwa 7 ga watan Febrairun 2021.

Sakataren Ma’aikatar kula da wasannin ta kasa Gabriel Aduda ya bayyana cewa sun nemi gwamnatin tarayya ta dauki nauyin wasan ne sakamakon rashin kudi da ma’aikatar tasu ke fama da shi.

Ya kuma bayyana cewa za a fara horarwas gwaji dan zabar yan wasan da zasu wakilci Najeriya a yayin kakar wasan, ya shaida cewa a filin wasan Ahmadu Bello na jihar Kaduna ne gwajin zai wakana a tsakanin 10 zuwa 13 na watan disamba din nan da muke ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply