Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi alkawarin bawa duk wani kwararren mai binciken kimiyya dan Najeriya da ya kirkiro rigakafin cutar Coronavirus zunzurutun kudi Naira Miliyan 36.
Shugaba Muhammadu Buharin Nijeriya
Ministan Kimiyya da Fasaha ta kasar, Dakta Ogbonnaya Onu ne ya yi wannan alkawarin a Abuja a wurin bikin yaye daya daga cikin direktocin ma’aikatar, Injiniya A. Oyefeso da ya yi ritaya daga aikin gwamnati.
Onu ya ce akwai bukatar Najeriya ta fara tunani mai zurfi da hangen nesa domin ta kare mutanen kasar daga kamuwa da cutar da Corona.
Ya ce gwamnati za ta rika bawa masu binciken kimiyya a kasar tallafi domin a taimaka musu su rika kirkirar magunguna domin magance cututtukan da ke adabar mutanen kasar.
