Home Labarai Nijeriya za ta dawo da ‘yan gudun hijra daga Chadi

Nijeriya za ta dawo da ‘yan gudun hijra daga Chadi

113
0

A Larabar nan ne shugaban kasar Chadi Idriss Beddy ya gana da wakilan Nijeriya cikinsu harda gwamnan jihar Borno Babagana Umar Zulum da jakadan Najeriya a kasar ta Chadi Zannah Umar Bukar Kolo kan yadda za a dawo da dubban ‘yan gudun hijira ‘yan Najeriya zuwa gida.

Mai magana da yawun gwamna Zulum, Isa Gusau ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa inda yace an yi ganawar ne domin ganin yadda za a dawo da ‘yan gudun hijirar gida bayan guduwarsu sakamakon hare-haren ‘yanta’adda tun cikin shekarar 2014.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa sun je kasar ta Chadi ne don ganin mutanensu, su gode wa gwamnatin kasar ta Chadi sannan kuma su shirya yadda za su dawo da mutanen gida cikin salama.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply