Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya ce majalisar zartaswar Nijeriya ta amince da gina kamfanonin ƙera takalma, sutura da sarrafa fatu a Janguza da ke jihar Kano da kuma Aba, a jihar Abia ƙarƙashin tsarin haɗin guiwar gwamnati da kamfanoni.
Aregbesola wanda ya faɗa wa ƴan jaridar fadar shugaban ƙasa haka, bayan taron majalisar zartaswar da shugaba Buhari ya jagoranta, ya ce kamfanin Nijeriya ne zai gudanar da aikin tare da tallafawar wani daga China.
Ministan ya ce aikin, wanda zai laƙume Naira Biliyan ₦5.1 zai samar da ayyukan yi kimanin 4,330.
