Home Labarai Nijeriya za ta gina sabbin filayen jiragen sama

Nijeriya za ta gina sabbin filayen jiragen sama

229
0

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta gina sabbin filayen jiragen sama guda 10 a fadin kasar ta yadda za a kara bunkasa bangaren sufurin samar kasar.

Ministan sufurin sama Sanata Hadi Sirika ne ya bayyana haka a Abuja yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin ma’aikatar ga kwamitin majalisar dattawan Nijeriya.

Hadi Sirika ya ce sufurin samar Nijeriya zai kara samun tagomashi matukar aka gina wadannan sabbin filayen jirage guda 10.

Ya kara da cewa tuni aka fara aikin filayen jiragen sama na Warri da ake yi a Osubi da kuma na Jigawa da Kebbi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply