Home Labarai Nijeriya za ta haɗa guiwa da Kamaru da Chadi don yaƙar ta’addanci

Nijeriya za ta haɗa guiwa da Kamaru da Chadi don yaƙar ta’addanci

52
0

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta hada guiwa da dakarun kasashen Kamaru da Chadi domin kawo karshen ta’addanci a Arewa maso Gabashin kasar nan.

Babba Hafsan Sojin Nijeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana haka lokacin da yake yi wa ‘yan jarida bayani ranar Litinin, a sansasin sojoji na Ngamdu da ke jihar Yobe.

Hakama ya bada tabbacin walwalar dakarun da ke aiki a yankin na Arewa maso gabas, yana mai cewa yanzu haka ana kokarin siyo takalma, kaki da kayan kariya da za a ba sojojin nan da makonni masu zuwa.

Ya kuma bukaci dakarun su kara kaimi wajen fatattakar ‘yan Boko Haram, yana mai cewa rundunar soji za ta samar da dukkan abun da dakarun ke bukata don jin dadin aikinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply