Home Labarai Nijeriya za ta kashe ₦126bn don inganta ɓangaren kiwon lafiya

Nijeriya za ta kashe ₦126bn don inganta ɓangaren kiwon lafiya

153
0

Ƙaramin Ministan kasafi da tsare-tsare Prince Clem Agba ya ce gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan ₦126 daga tsarin inganta tattalin arziƙi domin inganta kayan kiwon lafiya a asibitoci ƙwararru FMCs da kuma asibitocin koyarwa ta hanyar gina ɓangarorin bada cikakkiyar kulawa ICU.

Haka ma cibiyoyin gwaji da na killace marasa lafiya da ke jihohi 36 na ƙasar da Abuja, za su amfana da shirin.

Ministan wanda ya bayyana haka a lokacin taron wata gidauniyar bada tallafi ta TAHF, ya ce gwamnati a shirye take wajen inganta ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply